1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsin lamba ta kafafen sada zumunta

October 29, 2020

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu gagarumin ci gaba a kokarin samar da tsaro a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da ke fama da matsalar masu kisan ba gaira.

Nigeria Katsina Sicherheit
Matasa sun yi zanga-zanga kan matsalar tsaro a Arewacin NajeriyaHoto: DW/H. Y. Jibiya

Kasa da 'yan kwanaki ke nan dai da yakin neman tabbatar da samar da tsaro a sashen arewacin Najeriyar ta kafafen sada zumunta, da nufin karkatar da hankalin mahukuntan kasar ya zuwa neman mafitar rashin tsaron tsaron da ya mamaye sassa dabam-dabam a yankin na Arewa. Ko a makon da ya shude dai 'yan ina da kisan sun hallaka kimanin mutane 20 a Zamfara ko bayan sace kusan 50, a wani abu da ke nuna irin girman rikicin na 'yan ina da kisa da ke kama da dashi mai rai guda tara.

Karin Bayani: Najeriya: Mallakar bindiga domin kariya

To sai dai kuma Abujar ta ce ta samu gagarumi na ci gaba a kokari na kai karshen rashin tsaron a jihohin Arewa maso Yamma da suka hadar da Katsina da Zamfara da ma sashen Arewa ta Tsakiyar Najeriyar kamar Niger da Nasarawa.

Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Shugaban Mohammad Buhari  dai yace kaddamar da jerin kamfen din soja cikin yankunan guda biyu ya sake kaiwa ga zama na lafiyar da ake da bukata a sashen arewacin kasar: "Kasarmu mai albarka ta fuskanci kalubale iri-iri na tsaro tun daga samun 'yancin kanta. Wannan barazanar rashin tsaro yai tasiri ga  harkoki na kasuwa da samun jari da lafiya da ma ilimin al'ummarmu. Amma ina farin cikin fadin cewar an cimma da dama ga batun tsaron tsaron cikin gida a sassan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda aka kaddamar da jerin kamfen din soja iri na hadaran daji da harbin kunama da tsaftace Sahel da kuma guguwa. Wannan ya samar da komawar lamura daidai a wasu daga cikin yankunan."

Karin Bayani: Najeriya: Kakkabe 'yan bindiga a Katsina

To sai dai kuma in har Abujar tana karatun nasara a yankunan, daga dukkan alamu mazauna na yankunan na fadin da sauran tafiya a kokari na tabbatar da bacci idanu a rufe.  Hon Bello Matawalle na zaman gwamnan jihar Zamfara da kuma ya ce jihar tana da bukatar kari na jami'an tsaro da nufin kare 'ya'yanta da ke fuskantar karuwar hari daga masu sana'ar ta kisa.