Gwamnatin Amurika ta maida martani ga amsar da Iran ta ba Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia i
August 24, 2006Fadar gwamnatinAmurika, ta bada sakamakon nazarin da ta yi, ga amsar da Iran ta ba komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, a game da rikicin makaman nukleya.
Amurika ta ce, ba ta gamsu da wannan amsa ba, ta la´akari da, ƙarancin bayyani da ke cikin ta.
To saidai fadar White House ,ba ta anbaci batun saka takunkim ba ga Iran.
Sanarwar da Amurika ta bayyana, ta ce amsar da Iran ta bada,, ba ta cika sharruɗan da komitin sulhu ya gindaya ba, wanda su ka umurci hukumomin Teheran, su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa , ta hanyar wasti kwata- kwata, da batun ƙera makaman nuklea.
Kakakin fadar White House, Gonzallo Gallegos, ya ce gwamnatin Bush, ta fara tantanawa da sauran ƙasashen membobin komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, domin cimma daidaito, a kan mataki na gaba, da ya kamata a ɗauka, a cikin wannan baddaƙala.
Amurika, ta bukaci ƙasashen su haɗa kai, su kuma yi magana da murya ɗaya, don cilastawa hukumomin Teheran bada kai bori ya hau.
Ranar 31 ga watan da mu ke ciki ne, a ke kai wa´adin ƙarshe, da komitin sulhu ya ba Iran, na yin watsi da shirin ta, na ƙera makaman nuklea.