Gwamnatin Borno ta sama wa malamai gidaje
October 9, 2025
Gwamnatin jihar Borno, ta raba gidaje da aka gina musamman domin malaman makaranta a yankunan karkara, da nufin karfafa gwiwarsu don su zauna su samar da ilimi.
Gidajen da aka gina a wasu kanan hukumomin jihar sun kunshi gine-gine masu hawa uku, dauke da dakunan kwana biyu zuwa uku, tare da dukkanin abubuwan more rayuwa da suka dace.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa malamai su ne ginshikin ci gaban al'umma. Kuma idan ba su da kwanciyar hankali, ba za su iya ba da ilimi mai inganci ba.
Wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin jihar na farfado da ilimi a yankunan da suka fuskanci tashe-tashen hankula, tare da tabbatar da cewa malamai suna da wurin zama mai kyau da aminci.
Malaman da suka ci gajiyar wannan shiri sun nuna farin ciki da godiya, suna mai cewa hakan zai saukaka musu matsalolin rayuwa da aiki.