1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamnatin Burkina Faso ta rufe fitaccen gidan rediyon kasar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 2, 2025

Wasu da aka dakatar sun hada da LCI ta Faransa da RFI da kuma France 24, sai wasu na cikin gida, yayin da kuma aka tilasta wa 'yan jarida da dama yin gudun hijira.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore
Hoto: Mikhail Metzel/AFP

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta rufe fitaccen gidan rediyon kasar mai suna Radio Omega, ta hanyar dakatar da lasisin aikinsa ranar Asabar, sakamakon samunsa da laifin ayyana gwamatin kasar a matsayin ta karfa-karfa, a ranar 30 ga watan Yulin 2025.

Karin bayani:Harin 'yan bindiga ya kashe sojojin Burkina Faso 50

Hukumar kula da harkokin yada labaran kasar ta sanar da cewa dakatarwar ta watanni uku ce, inda gidan rediyon ya shiga sahun kafafen yada labaran da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore ta dakatar, tun bayan darewa kan karagar mulki a cikin watan Satumban shekarar 2022.

Karin bayani:An saki mai caccakar gwamnatin Burkina Faso

Wadanda aka dakatar sun hada da LCI ta Faransa da RFI da kuma France 24, sai wasu na cikin gida, yayin da kuma aka tilasta wa 'yan jarida da dama yin gudun hijira sakamakon yanayin aikinsu.