SiyasaAfirka
Chadi: Rikicin kabilanci ya janyo mutuwar mutane 42
March 21, 2024Talla
Gwamnatin Chadi ta tabbatar da mutuwar mutane 42 sakamakon rikici tsakanin kabilu biyu na gabashin kasar, tare da jikkatar wasu da dama.
Karin bayani:Chadi: Sojoji sun kashe babban dan adawa
Ministan tsaron kasar Janar Mahamat Charfadine Margui, ya ce sun samu nasarar cafke mutane 175 da ke da hannu wajen aikata kisan, bayan sun kona kauyen Tileguey na lardin Ouaddai, wanda ya yi kaurin suna wajen rikicin makiyaya da manoma. Kuma mutane da dama a garin sun mallaki bindigogi.
Karin bayani:Hari a Chadi ya hallaka mutane da dama
Manoman dai na zargin makiyaya da tura dabbobinsu cikin gonaki suna lalata musu shuka.