1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin haɗin kan ƙasa a Nepal

April 1, 2007

A wani mataki na kawo ƙarshen rikicin tawaye, an cimma nasara girka gwamnatin haɗin kan ƙasa a Nepal, wadda ta ƙunshi yan tawayen masu aƙidar Mao.

Shugaban rundunar tawayen, Perachanda ya ce wannan rana ta kasance tarihi a ƙasar, ta la´akari da tubalin tushen da a ka girka cikin ta, na samar da zaman lahia mai ɗorewa a ƙasar Nepal, bayan shekaru 10 na yaƙin bassasa, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 13.

Sabuwar gwamnati ta ƙunshi minsitoci 5, na ƙungiyar tawayen Mao.

Domin cigaba da ƙarfafa wannan ƙwarya-ƙwaryan zaman lahia, ɓangarori masu gaba da juna a ƙasar Nepal, sun tsaida ranar 20 ga watan juni , domin shirya zaɓen yan majalisar dokoki.

Shugaban tawayen, ya alƙawarta rikiɗa ƙungiyar sa, a matsayin jama´iyar siyasa, wadda a cewar sa, zata bada gudun muwar da ya dace, a ci gaban wannan ƙasa.

Saidai har yanzu, yan adawar na tsaye kann bakan su a game da batun maiyar da gidan sarautar Nepal saniyar ware, a game da harakokin mulki.