1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Kafa gwamnatin hadaka a Saxony

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 18, 2024

Nasarar da jam'iyyar AfD ta masu tsattsauran ra'ayin kyamar baki ta yi a zaben jihar Saxony da ke gabashin Jamus, ya tilasta kafa gwamnatin hadaka.

Jamus | Saxony | Zabe | AfD | SPD | CDU/CSU
A watan Satumbar 2024 ne, aka gudanar da zabe a jihar Saxony da ke gabashin JamusHoto: Matthias Rietschel/REUTERS

Nasarar da ta AfD dai, ta tilasta jam'iyyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya ta CDU/CSU kafa gwamnatin hadaka ta marasa rinjye da jam'iyyar adawa ta SPD. Yayin zaben da aka gudanar a watan Satumbar wannan shekara, jam'iyyar AfD ko dai ta samu nasarar lashe zaben ko kuma ta zo ta biyu a duka zabuka ukun da aka yi a gabashin Jamus. Wannan lamarin dai, ya hana duka manyan jam'iyyun biyu na SPD da CDU damar samun rinjaye a majalisar dokoki ta Saxony. A yanzu wadannan manyan jam'iyyun na zaman doya da manja, gabanin zaben kafin wa'adi da za a gudanar a watan Fabarairun shekara mai zuwa ta 2025 bayan rushewar gwamnatin hadakar kasar. Amma nasarar AfD a jihar ta Saxony, ta tilasta musu kafa gwamnatin hadaka mara karsashi.