1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Jamus na cikin tsaka mai wuya

Scholz Kay-Alexander USU
June 15, 2018

Gwamnatin Jamus na fuskantar mummunan wadi na tsaka mai wuya inda aka samu sabanin ra'ayi kan yan gudun hijira tsakanin jam'iyyun CDU CSU da suka dade su na kawance da juna.

Bundeskanzlerin Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber

Wannan sabani dai babban abin da ya jawo shi ne batun 'yan gudun hijira inda shugabar gwamnati Angela Merkel ta dage cewa dole a ci gaba da karbabn baki, kamar yadda aka cimma yarjejeniya da sauran kasashen Turai shi kuma ministan cikin da Seehofer ya ce sai a rika dakatar da yan gudun hijirar tun daga kan iyakar kasar Jamus don hana musu shigowa cikin kasar.

Sai dai Merkel ta jaddada cewa ba zai yiwu Jamus ta juya baya yayinda wasu kasashen Turai ke fuskantar matsala a kan 'yan gudun hijirar ba domin matsalar da ta shafi kasa daya ta shafi dukkan kasashen Turai.

Hoto: Imago/Ipon

Sai dai kuma ministan cikin gida Horst Seehofer, so yake Jamus ta dauki matakn kashin kanta, babu ruwanta da abinda ya shafi Turai, matakin da Merkel ta sa kafa ta shure.

Wannan sabanin da ya kunno kai tsakanin Merkel ta jam'iyyar da suke aminci, ba karamin tashin hanakali ya kawo tsakanin 'yan siyasa ba, domin a tarihin Jamus sama da shekaru 30 a ba'a taba ganin irin wannan rudani ba.

Sabani tsakanin CSU da CDU tamkar fadan cikin gida ne, ba wai fada tsakanin jam'iyya mai mulki da wata jam’iyyar adawa ba.

Idan har ba samu maslaha ba, to hakan na iya sa gwamnatin ta rushe baki daya.

Su kansu 'yan siyasar na bangarorin biyu sun  kwan da sanin hatsarin da rikicin ka iya jawo wa.