1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Gwamnatin Jojiya ta ki gudanar da tattaunawa da 'yan adawa

Mouhamadou Awal Balarabe
December 2, 2024

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da masu zanga-zanga a Jojiya suka sake taruwa a rana ta biyar a gaban majalisar dokokin da ke birnin Tbilisi, domin yin tir da matakin dakatar da shirin shiga cikin kungiyar EU.

Masu zanga-zanga na neman gwamnati ta lashe amanta na kin shigar da Jojiya cikin EU
Masu zanga-zanga na neman gwamnati ta lashe amanta na kin shigar da Jojiya cikin EUHoto: Zurab Tsertsvadze/AP/picture alliance

Firayiministan Jojiya ya ki amincewa da duk wata tattaunawa da 'yan adawan kasar domin gudanar da sabon zaben 'yan majalisar dokoki bayan zargin tafka magudi. Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da dubban masu zanga-zangar suka sake taruwa a rana ta biyar a gaban majalisar dokokin da ke birnin Tbilisi, domin yin tir da matakin da hukumomi suka dauka na dakatar da shirin shiga cikin kungiyar EU.

Sai dai a kokarinsa na yayyafa ruwan sanyi ga jerin zanga-zangogi, Firayiminista Irakli Khobadidze ya lashe amansa inda ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi kokarin shigar da Jojiya cikin Kungiyar Tarayyar Turai, makon guda bayan da ya dakatar da shirin zama mamba na EU. Sannan ya yi amfani da taron manema labarai da ya gudanar wajen zargin kasashen waje da katsalandan na al'umaran cikin gida, lamarin da a cewarsa ba za a yi kai ga haifar da juyin juya hali a Jojiya ba.

 Jam'iyyar da ke rike da kan madafun ikon Jojiya tun 2012 na shan zargi daga 'yan adawa na dasawa da Rasha, yayin da jami'an da ke mulki ke zargin kasashen yammacin duniya da neman jefa Jojiya cikin yaki da Rasha.