Gwamnatin kasar Masar ta yi murabus
February 24, 2014Wata sanarwa ce da aka fitar da tsakiyar ranar wannan Litinin din (24.02.2014), ta tabbatar da wannan labari, inda sanarwar ta kara da cewa gwamnatin ta yi murabus din ne, dangane da yanayin da kasar ta ke ciki a yanzu.
Murabus din Gwamnatin ta Masar ya faru ne 'yan makonni kafin zaben shugaban kasar da za'a yi a.
Babban kwamandan sojojin kasar ta Masar Marshal Abdel Fattah Al-Sissi, ministan tsaro, kuma mataimakin Firaministan a gwamnatin da ta yi murabus, bai boye aniyarsa ta son tsayawa takara a zaben shugaban kasar ba, sai dai kuma idan yana so ya zama dan takara, sai ya yi murabus daga gwamnati, sannan ya ajiye kakinsa na soja kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Tun dai kafin sanarwar murabus din ce, Firaministan kasar Hazem el-Beblawi, da sojojin suka nada shi bayan kifar da gwamnatin shugaba Mohammed Morsi, ya sanar da yiwuwar murabus din yayin wata hira da 'yan jaridu da ya yi da kuma aka watsa kai tsaye ta gidan Talabijin na kasar ta Masar.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Usman Shehu Usman