Gwamnatin kawance a Nijar na janyo rudani a jam'iyyar MNSD
August 13, 2013 A lokacin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Yamai, biyo bayan wani taron gaggawa da ya shirya, kwamitin zartarwar jam'iyyar ta MNSD NASARA, madugar kawancen jam'iyyun adawar kasar na ARN, ya jaddada matsayin jam'iyyar na yin watsi da tayin
shugaban kasar na shiga gwamnatin hadin kan kasa, tare kuma da nisanta kansa daga sanarwar da 'yan majalisar dokokin 7 na jam'iyyar suka fitar, kamar dai yanda malam Mrtala Alhaji Mamuda, sakataren yada labarai na jam'iyyar ta MNSD ya yi mana karin bayani.
Shima dai daga nashi bangaren, rukunin 'yan majalisar dokoki na
jam'iyyar ta MNSD NASARA a majalisar dokokin kasar ta Nijar, ya kira taron manema labarai inda ya mayar da martani a kan sanarwar da bijirarrun 'yan majalisar suka fitar. Honourable Abdulkadri Tijjani, shi ne shugaban rukunin 'yan majalisar dokokin na jam'iyyar ta MNSD, kuma a cewarsa, basu san da wannan matsayin ba.
Sabanin ra'ayin 'yan majalisa a kan shiga gwamnati
Sai dai a share daya kuma, 'yan majalisar jihar Maradi su biyar wadanda suka kasance daga cikin jerin 'yan majalisar dokokin jam'iyyar ta MNSD NASARA 7 da suka fitar da sanarwar goyon bayan shigar jam'iyyar tasu a cikin gwamnatin hadin kan kasar ne su ka yi amai suka lashe, kamar dai yanda za ku ji a hirar da ta hadani da Honourable Haruna Dan Labo, wanda ya ke daya daga cikinsu.
Sai dai daga nasu bangare, sauran 'yan majalisar dokokin jam'iyyar ta MNSD NASARA na jiihar Tawa, da suka fitar da sanarwar goyon bayan tayin shugaban kasar, sun ce su kam suna nan a kan bakansu.
Yanzu dai za a iya cewa a hankali wannan batu na kafa gwamnatin hadin kan kasa na kara tabbatar da barakar da ta soma kunno kai a cikin jam'iyyar MNSD NASARA, wacce a yau ta shiga wani hali na mai abu ya rantse maras abu ya rantse a tsakanin 'ya'yanta.
Mawallafi : Gazali Abdou Tasawa
Edita : Saleh Umar Saleh