Gwamnatin Kibaki a Kenya ta fada cikin halin kaka ni kayi
December 8, 2005Da yawa daga cikin yan jamiyyun adawa a kasar Kenya sunki amincewa da goron gayyatar da shugaba Mwai Kibaki ya kima musu na shiga cikin sabuwar gwamnati ta hadin gwiwa.
Rahotanni sun shaidar da cewa daga cikin madafun ikon da dada yawa daga cikin yan jamiyyun adawar suka ki amincewar akwai ofisoshin ministoci guda biyu da kuma mataimakan su guda 13.
Mutanen dai da suka ki karbar goron gayyar sun fito ne daga jamiyyar ta Shugaba Kibaki, wato NRC da kuma ta yan adawa , wato FKP.
Daga dai tun lokacin da kasar ta samu yancin kai daga turawan Ingila a shekara ta 1963 ,ba a taba fuskantar yanayi na inda yan siyasa suka yi watsi da goron gayyatar karbar mulki ba sai a wannan karo.
Wannan dai sabon al´amari a yanzu haka ya kara tsunduma gwamnatin ta Kibaki a cikin hali na kaka ni kayi, bayan gagarumin rashin amincewar da shirin sa na gyaran tsarin mulki ya samu ta hanyar zaben raba gardama da aka gudanar.