Gwamnatin Kwango ta yi watsi da kiran sake zaben kasar
December 28, 2023Kakakin gwamnatinkasar Kwango Patrick Muyaya ya sanar da hakan duk da kiran da 'yan adawa suka yi na a sake gudanar da zaben mai cike da takaddama.
Kwarya-kwaryar sakamakon zaben na ranar 20 ga watan Disamba a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango, ya nuna shugaba Felix Tshisekedi yana kan gaba da yawan kuri'u a kan 'yan adawa.
Tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kan zaben na barazanar kara dagula lamura a Kwangon, wadda tuni ke fama da matsalar tsaro a yankunan gabashin kasar, da ke da dumbin arzikin ma'adanai da karafa na masana'antu a duniya.
'Yan sanda sun yin amfani da karfi wajen tarwatsa wata zanga-zangar adawa da aka haramta gudanarwa a Kinshasa babban birnin kasar, in da jama'a suka yi dafifi don nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, da a cewarsu ke cike da kura-kurai.