Tsaikon tattaunawar tsagaita a wuta a Libya
February 19, 2020Janyewar gwamnatin ya biyo bayan hare haren rokoki a wata tashar jiragen ruwa a birnin Tripoli, wurin da tsawon watanni madugun tawaye Khalifa Haftar ya hara domin kawar da gwamnatin daga karagar mulki.
Harin na baya bayan nan na daga cikin sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Janairu tsakanin Rasha wadda ke goyon bayan Haftar da kuma Turkiyya da ke goyon bayan gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.
A cikin wata sanarwa gwmnatin Libya ta fitar ta zargi Haftar da yunkurin lalata kasar bayan da ya gaza cimma burinsa na hambarar da ita.
A ranar Talata jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Libya Ghassan Salame ya kaddamar da zagaye na biyu na tattaunawa a yunkurin kasashen duniya na kawo karshen fada tsakanin bangarorin biyu.
Tun a shekarar 2011 Libya ta fada tashe tashen hankula bayan hambarar da Moamar Gaddafi inda bangarorin 'yan bindiga kowanne ke hankoron kwace madafan iko.