1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Lucas Papademos ta kama aiki a Girka

November 11, 2011

Sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasa a Girka tayi alkawarin warware matsalolin bashi da ya durkusar da tattalin arzikinta

Lucas PapademosHoto: picture-alliance/dpa

A yau ce aka naɗa  gwamnatin haɗin kan kasa a karkashin jagorancin Lucas Papademos, da nufin ceto Girka daga basussukan da suka jagoranci karayar tattalin arzikin kasar. Sabon Priministan Girkan ya sanar da cewar, sabuwar gwamnatin zata yi iyakar kokarinta na warware matsalolin Girka.

 " Hanyar warware waɗannan matsaloli ba masu sauki ba ne. Amma na hakikance cewar zamu cimma burimmu. Za mu yi iyakar ƙoƙarinmu na gaggauta shawo kan matsalar, amma hakan na bukatar haɗin kan kowa da kowa da kuma aiki kafaɗa da kafaɗa".

An sanar da sabuwar gwamnatin Girkan ne da barin Evangelos Venizelos a mukaminsa na ministan harkokin kuɗi. Ɗan siyasan jam'iyyar sassaucin ra'ayin kaza lika zai ci gaba da rike mukaminsa na mataimakin Priminista. Sabuwar majalisar zartarwar dai ta ƙunshi wakilai daga manyan jam'iyyun ƙasar biyu, da kuma sauran ƙananan jam'iyyu na Girkan.  Bayan kai ruwa rana na tsawon kwanaki huɗu ana mahawara, a jiya alhamis ce manyan jam'iyyun ƙasar  suka cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, akarkashin jagorancin Lucas Papademos.  Ana saran zai jagorancin sabuwar gwamnatin na rikon ƙwarya, zuwa lokacin da za'a gudanar da zaɓe a shekara mai zuwa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar

Edita          : Umaru Aliyu