Gwamnatin mai ci a Pakistan na rawa
January 12, 2012A kasar Pakistan gwamnati Asif Ali Zardari na cikin tsaka mai yuwa, kan batun wata wasika da ya rubutawa kasar Amirka da ta kare shi daga juyin mulkin sojoji, wanda kuma aka tseguntata. An dai yi ta rade-radin cewa Zardari zai sauka daga mulki tun dawowa daga jinya a Dubai. A jiya an sallami ministan tsaro kuma babban kusa a sojojin kasar masu iko mai karfi a Pakistan. A yau babban hafsan hafsoshin kasar ya kira taron kwamandojin sojin kasar don ganawar gaggawa, wata majiyar soji tace, suna son Zardari ya sauka daga mulki, amma ta hanyar doka ba juyin mulkin soji ba. Yanzu haka dai kotun kolin kasar na bincike kan wasikar da ya rubutawa Amirka, kuma tabbas in an samu shugaban da laifi to zai sauka daga mulki, haka ma kotun na binciken wasu manyan jami'ai a jam'iyar shugaba ciki har da firayim ministan Yusfu Raza Gilani, wadanda za a iya saukar da su, idan aka same su da laifi. A kasar Pakistan dai sojoji na da karfin fada aji, kuma basa barin duk wani dan siyasa ya shiga harkarsu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu