1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamnatin Mali ta tsawaita wa'adin shugabancin Janar Goita

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 12, 2025

Janar Goita ya rushe dukkan jam'iyyun siyasar kasar, duk da alkawarin da ya yi na mayar da Mali kan turbar Dimukuradiyya

Shugaban Mali Janar Assimi Goita
Hoto: Ken Ishii/POOL/AFP

Fadar mulkin gwamnatin sojin Mali ta amince da kudurin tsawaita wa'adin shugabancin Janar Assimi Goita har na tsawon shekaru biyar masu zuwa, wato shekarar 2030, ba tare da gudanar da wani zabe ba.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne Janar Goita ya rushe dukkan jam'iyyun siyasar kasar, har ma da kungiyoyi masu zaman kansu, duk kuwa da alkawarin da ya yi a bara, na mayar da mali kan turbar Dimukuradiyya.

Karin bayani:Ficewar Wagner daga Mali ba ta bata alakar Rasha da Afirka ba

Tun a shekarar 2012 Mali ta fada cikin tashe-tashen hankula na kungiyoyi masu ikirarin jihadi, wadanda ke da alaka da Al-Qaeda da IS, da ma wasu kungiyoyin ta'addanci, kuma suke ta halaka jama'a a hare-haren da suke ta kai wa lokaci zuwa lokaci.