1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Masar ta yi murabus

January 29, 2011

Shugaba Hosni Mubarak ya rusa gwamnatinsa a hukumance kamar yadda ya alƙawarta wa al'umar ƙasarsa.

'Yan zanga-zanga na ci gaba da kira ga Hosni Mubarak da ya yi murabusHoto: AP

Gwamnatin Masar ta yi murabus a hukumance sakamakon boren da ake ci gaba da yi a faɗin ƙasar. Ɗokacin jami'an gwamnatin shugaba Hosni Mubarak sun ba da takardunsu na yin murabus a wannan Asabar, bayan da shugaban mai shekaru 82 da haifuwa ya yi wa Masarawa alƙawarin rusa gwamnatinsa. To amma Mubarak ya ƙi ya sauka daga karagar mulki yana mai kunnen uwar shegu ga 'yan zanga-zangar da ke cewa ba za su daina ba har sai ya yi murabus. Dubban 'yan zanga-zangar ne dai suka yi dafifi a babban dandalin da ke birnin AlƘahira inda aka girke sojoji. Gidan telebijan Aljazeera ya ba da rahoton da ke nuni da cewa sojoji sun tsawaita dokar hana fitan dare daga ƙarfe huɗu na yamma, domin kwantar da ƙura. Rahotanni sun yi nuni da mutuwar mutane 95 da suka haɗa da 'yan zanga-zanga da 'yan sanda tun bayan ƙaddammar da zanga-zangar a ranar Talatar da ta gabata. Sarki Abdullahi na Saudi Arebiya ya nuna goyon bayansa ga shugaba Hosni Mubarak tare da kiran boren tamkar matakin da bai dace ba.

Mawalafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal