1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta kori kungiyoyin ketare masu ayyukan jin kai

Gazali Abdou Tasawa MAB(AMA
November 13, 2024

Gwamnatin mulkin soja a Nijar ta soke takardar izinin aikin wasu manyan kungiyoyi masu zaman kansu da ke gudanar da ayyukan jin kai a kasar ciki har da kungiyar ACTED ta kasar Faransa.

Shugaban majalisar koli ta mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani da mukarabansa
Shugaban majalisar koli ta mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani da mukarabansaHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

Kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin mulkin sojan kasar Nijar suka dakatar da aikin nasu sune kungiyoyin ACTED ta kasar Faransa wacce ta soma aiki a Nijar tun a shekara ta 2010, inda take gudanar da ayyukan jin kai kamar a fannin kula da ‘yan gudun hijira a yankunan da ke fama da matsalar tsaro. Kungiyar  ACTED na kunshe da ma'aikata 271 daga ciki 253 ‘yan Nijar. Ta kuma yi ikirarin kawo taimako ga mutane sama da 210 a shekarar 2023 a karkashin wasu muhimman ayyukan da ta yi a fadin kasar.

Ita kuwa kungiyar Action pour le bien etre wato (APBE) kungiya ce mai zaman kanta da wasu ‘yan Nijar suka girka a shekarar 2009, ta kuma ke gudanar da ayyukan jin kai a fannin kula da lafiyar mata da kananan yara, tana yaki da cutar SIDA da ta tamowa, kungiyar ta kuma kawo tallafi ga mutanen da wani iftila'i ko yaki ya saka a halin ha'ula'i, da kuma taimakawa a fannin noman rani da kafa rumbunan tsimin cimaka, kana kungiyar na taimako a fannin kiwo wajen yi wa dabbobi shaushawa da kuma samar da wuraren ban ruwan dabbobi.

Matan da kungiyoyi masu zaman kansu ke taimakawa wajen yaki da gurgusowar hamada a NijarHoto: Fatoumata Diabate/Oxfam

Karin bayani : Nijar: Bukatun al'umma a kan gwamnati

A kudirin doka da ma'aikatar cikin gidan Nijar ta dauka ta soke takardar izin aikin wadannan kungiyoyi masu zaman kansu biyu, matakin da Malam Bana Ibrahim na kungiyar Front Patriotique mai goyon bayan mulkin soja ya ce ya yi daidai, yana mai cewa "Matakin da gwamnati ta dauka bai shafi dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu ba. Wadanda ba sa bin ka'ida su ne gwamnati ta janye wa wannan izini. Kuma ka san tun bayan juyin mulki na ranar 26 ga watan Yulin 2023 abubuwa sun sauya a cikin kasarmu. Ba ma yarda kuma mahukuntan Nijar ba sa yarda wani ya zo da sunan taimako ko tallafa wa talakawa ya bai wa wata kasa damar ta yi leken asiri a cikin kasarmu."

To amma wasu ‘yan Nijar na nuna damuwa dangane da abin da suka kira illar da ke tattare da wannan mataki da zai raba daruruwan yan kasar da aiki da kuma dubunnan ‘yan kasa da taimakon agajin da suke samu daga wadannan kungiyoyi kamar su Malam Changa Tchalimbo wanda ke daga cikin masu irin wannan damuwa. "A shekara daya da rabi kimanin kungiyoyi masu zaman kansu 200 aka soke a Nijar, kuma wadannan kungiyoyin ma'aikatan nasu wani irin mataki gwamnati ta dauka na sama masu wani aikin? Domin suna da iyalai da suke ciyarwa, kuma maganar gaskiya ni ina ganin babu wata maganar samun ‘yancin kai da ta wce mutum ya samu aikin yi."

Karin bayani : Nijar ta farfado da horon soja ga masu yi wa kasa hidima

Kungiyoyin agajin na kasa da kasa na taimakon matan karkara da ruwan shaHoto: IRC

Sai dai  Malam Soule Oumarou na Kungiyar FCR na ganin akwai bukatar gwamnatin ta fito ta yi wa ‘yan kasa bayani game da dalilanta na daukar wannan mataki kan wadannan kungiyoyin, inda ya ce "Wadannan kungiyoyi akwai wani laifi da suka yi takamaimai da ya sa aka soke su ko kuma akwai zagon kasa da suke yi a cikin kasa. Ya kamata gwamnati ta fito ta yi bayani domin kungiyoyi ne da ke kawo gudunmawa ga talakawa, ‘yan kasa na cin amfaninsu kuma ‘yan kasa da yawa ke aiki a cikinsu."

Gwamnatin mulkin sojan kasar Nijar ta sanar da ci gaba da gudanar da binciken ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu na ciki da wajen kasar domin daukar mataki a kan duk wacce za ta samu tana tafiyar da ayyukan nata ba a kan ka'idar sabuwar tafiyar Nijar ba.