1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin mai ya zo karshe a Najeriya

April 7, 2020

A wani abun da ke zaman ta leko tana shirin komawa a cikin Tarayyar Najeriya, bayan ragin farashin man fetur har sau biyu cikin makonni biyu, kamfanin mai na kasar ya ce an cire tallafin da ke cikin masana'antar.

Erdölindustrie in Nigeria
Kawo karshen tallafin man fetur a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/Göttert

Murna dai daga dukkan alamu tana shirin komawa cikin ciki a Tarayyar Najeriya da ta rage farashin man fetur har sau biyu cikin tsawon makonni guda biyu, amma kuma take neman kare tallafin cikin harkar man mai tasiri. Shugaban kamfanin man kasar na NNPC Mele Kyari dai ya ce daga yanzu kamfanin da ke akan gaba ga samar da daukacin fetur da kasar ke sha, zai mai da kasuwa alkali a cikin sayar da man ga 'yan kasa, abin kuma da ke nufin karshe na tallafi da gwamnatin kasar ke yi da nufin wadatar man fetur a daukacin kasar a farashi iri daya.

Kawo karshen sayen mai da arha

Alamu na kare tallafin dai ya faro tun daga makon jiya, sakamakon wani sabon farashin da hukumar kayyade farashin man fetur din ta fitar, amma kuma ta ce na zaman farashi na watan Afrilu kadai.

Yawan fasa bututun man fetur na kawo nakasuHoto: picture-alliance/A. Holt

Kare tallafin dai yana nufin kai karshen man fetur mai arha a cikin kasar da ta dauki lokaci tana cinikin hajar kasa da abin da ke akwai a farashi na kasuwanni na duniya. Zare tallafin dai na kuma iya kai wa ga ninka farashin man fetur cikin kasar a nan gaba, ga Najeriyar da ke zaman 'yar lele ko a makwabtan da suka dauki lokaci suna dogaro da man kasar domin harka ta rayuwa.

Nakasu gatattalin arzikin kasa

To sai dai kuma a fadar Lawal Habib da ke zaman masanin tattalin arzikin Najeriyar, sabon matakin na iya illa har ga tattalin arzikin kasar  bisa  rage mu'amala sakamakon tsadar makamashin man fetur a kasar.
Ko ya take shiri kayawa a tsakanin gwamnatin da ke neman rage batan kudi da suna na tallafin da ma al'ummar da ke ganin arhar fetur na iya kai wa ga rage tsada ta rayuwa da ma habakar ciniki, ga su kansu masu kwadagon kasar sabon matakin na kama da bindigar cikin ruwa ga Najeriyar ganin da kyar da gumin goshi ta kai ga sabon karin albashi a kasar.  

2012: Zanga-zangar adawa da cire tallafin mai a NajeriyaHoto: dapd

A baya dai an sha rikici a tsakani 'yan kwadagon da ke adawa da cire tallafin da ke da tasirin gaske ga rayuwar ma'aikatan kasar, kuma a wannan karo ma ana shirin a sake kwatawa a tsakanin ma'aikatan da ke fadin da sauran rina cikin kabar man fetur din da ke zaman na 'yan kasa, amma kuma babu moriya a cikinsa, a tunanin Kwamared Nasir Kabir da ke zaman sakataren kungiyar kwadagon kasar ta ULC. Har ya zuwa yanzu dai al'ummar kasar suna shan mai da arha sakamakon faduwar farashin danyen man a kasuwannin duniya, inda ake sayar da man fetur a kasar a kan farashin Naira 112 kan kowace lita.
 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani