1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Najeriya ta fadada hanyar samun kudin shiga

Ubale Musa SB/ZMA
December 6, 2023

Gwamnatin Najeriya ta yi gwanjon wani jirgin saman shugaban kasar, abin da ake gani sakamakon rikicin tattalin arziki da ake fuskanta ta hanyar neman kudin cike gibin kasafin kudin kasar..

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya lokacin gabatar da kasafin kudin 2023
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya lokacin gabatar da kasafin kudin 2023Hoto: Ubale Musa/DW

Duk da cewar dai ministan kudin kasar bai boye irin girman kalubalen tattalin arzikin da ke gaban 'yan mulkin Najeriya, batun karaurawa bisa jirgi na shugaban kasa dai daga duk alamu na can nesa cikin zukatun al'ummar Najeriya a halin yanzu. Kokari na gwanjon jirgin mai kirar Falcon 900B dai na kara fitowa fili da irin girman matsin da 'yan kasar ke iya  fuskanta a shekarar da ke shirin kamawa.

Karin Bayani: Najeriya: Kasafin kudin Tinubu na farko

A shekara ta 2015 dai tsohon Shugaba Muhammdu Buhari lokacin da yake rike da madafun iko ya ayyana aniya ta gwamnatinsa na rage yawan jiragen dake turaka ta shugaban kasar a cikin neman rage barna ta kudi kafin daga baya shugaban ya lashe amansa tare da jefa shawara cikin kwandon shara.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya lokacin gabatar da kasafin kudin 2023Hoto: Ubale Musa/DW

Kimanin jiragen sama 10 ne dai ke a karkashin iko na shugaban kasar, jiragen kuma da kan zama kafar alfahari ga jami'an gwamnatin da ragowar alfarma ciki har da wajen kasar. Wannan ne dai karo na farkon fari a shekaru kusan 20 da doriya da tarrayar Najeriyar ke kaiwa ga cefanar da jirage na shugaban kasa da zummar neman kudin biya na bukata. Kaftin Bala Jibril dai na zaman kwararre cikin masana'antar sufurin sama ta kasar, kuma ya ce da kamar wuya matakin ya yi tasirin rage radadin tattalin arzikin.

Gwanjon jirgin da ya share sheakru 33 yana hidima ga fada ta shugaban kasar dai, na kara fitowa fili da girma ta bukata ta kudin da ke gaban yan Mulki da ke da fata na burge 'yan kasar cikin takun mulki. Ana Shirin kare makon farko na Disamba ba tare da masu mulkin Najeriya biyan albashin watan Nuwamban daya shude ba, a wani abun da ke zaman ba sabunba a zuciyar ma'aikatan kasar.

Masu mulkin na Abuja dai sun dauki lokaci suna fadin sun gaji mataccen jaki a tattalin arzikin, kuma suna ganin baki a kokari na sake busa masa  rai domin amfanin miliyoyi na yan kasar dake zaman jira. Ko bayan jirgin dai ana saran  ciniki na kaddarori da yawa da nufin samun kusan triiliyan guda da Naira miliyan dubu 300 domin rage gibin da ke cikin kasafin na shekara mai kamawa. Yusha'u Aliyu dai na sharhi a tattali na arziki kuma ya ce ana bukatar kallon tsaf da nufin kaucewa wasoso bisa dukiyar al'umma a bangaren jami'ai na gwamnatin kasar. A cikin  halin rashi da ma alkawari na siyasa ne dai masu mulkin Najeriya ke fatan kaucewa muguwar rawa a farko na shekarun mulkinsu.