1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matakin ba sani ba sabo a kan barayin shanu

January 28, 2020

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce ba sani ba sabo a game da sabon hari da jiragen sama da ta tsara kai wa da nufin fatattakar barayin shanu a jihar Niger da ke tsakiyar kasar.

Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Gwamnatin Najeriyar ta ce, duk da cewar dai an kai ga tabbatar da sulhu a wasu jihohi irin Katsina da Zamfara, sannu a hankali barayin shanu da sace mutane sun sake taruwa a dazukan da ke a jihar Niger inda suke cin karensu ba babbaka. Lamarin da tuni ya kara tayar da hankulan dattawa na jihar da suka kai wa wata ziyara ga Shugaban kasar Muhammadu Buhari domin neman mafita.

Makiyaya na fuskantar barazana daga barayin shanu Hoto: Reuters/Goran Tomasevic

Tuni gwamnatin Najeriyar ta sanar da wani sabon kudurin amfani da jirage na sama da nufin cin dunduniyar barayin da ke a dazuka duk da dabarunsu na fahimtar aiyukan 'yansanda dama sojojin da ke kokari na kai karshen matsalar ta kasa.Tallafawa al'ummar Niger, ko sauyin sheka da barayin ke yi, dukkan alamu abun da ke faruwa a jihar Niger na zaman hijira ta barayin daga jihohi irin Katsina da Zamfara zuwa can Niger.

Gwamnatin Najeriya ta shirya fatatakar barayin shanu Kama daga Arewa zuwa Kudu, tarrayar Najeriyar dai na fuskantar wani sabon yanayin rashin tsaro ta ko'ina, inda yanzu haka wani sabon rahoto ya ambato ta a matsayin kasa ta uku da ke fuskantar matsalar a duniya ko bayan Afghanistan da Iraq.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani