1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta soke shirin kafa cibiyar masu fina-finai

Nasir Salisu Zango/AHJuly 25, 2016

Martanin da ya biyo baya a sakamakon daukar wannan mataki na soke gina katabaran cibiyar masu shirya fina-finai a Kano.

Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Matakin dai ya zama tamkar ta leko ta koma ga masu sana'ar shirya wasan kwaikwayo musamman ganin cewar ginin wannan katabaran sansanin na fina-finai zai kara musu martaba da kuma kwazo.Galibin al'umma sun soki lamirin shirin.Jami'in yada labarai na kungiyar masu shirya fina-finai na Kano Balarabe Murtala Baharu,ya bayyana cewar soke shirin bai zame musu asarasu ka dai ba, ta la'akari da irin tarin kudaden shiga da gwamnati ke samu daga garesu

Shi ma wani tauraro mai fitowa cikin fina-finan Hausa Mudansiri Haladu,ya ce sukar da wannan aiki ya samu baya na da nasaba da rashin wayar da kan mutane da gwamnati ta gaza yi a kan abin da ake nufi.Wasu malamai ne dai a kano suka nemi a soke wannan aiki bisa ra'ayin cewar sun gano hadarinsa,Malam Aminu Ibrahim Daurawa shi ne babban kwamanda Hisbah a Kano,kuma shararren malami mai wa'azi ya ce sune suka kira mataimakin shugaban kasa a kan harkokin majalisa suka kuma isar masa da sakon kin jinin wannan aiki.Yanzu haka dai an soke wannan aiki sai dai kuma duk da haka masu sana'ar fina-finai a Kano na jadadda rokonsu ga malamai da sauran al'umma da su rika yi musu kallon mutanen kirki maimakon yin Allah wadai da duk wani yunkuri da ya shafesu.