1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nijar ta rushe hukumar Fansho

Salissou Boukari
December 4, 2025

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da rushe hukumar kula da biyan kudadan fansho CARENI ta ma'akatan da suka yi ritaya.. A baya an sha fuskantar cece-kuce kan wannan hukuma

Nijar: Babban taron kasa
Nijar: Babban taron kasaHoto: Salissou Boukari/DW

A baya an sha faman cece-kuce kan wannan hukuma da ma tsarin biyan kudaden ‘yan fansho da suka yi ritaya, inda yanzu aka mayar da biyan kudadan a karshen kowane wata maimakon wata uku-uku da ake yi a baya.Tuni dai tsoffin ma'aikatan da masu sharhi suka soma mayar da martani kan wannan mataki. 

Shi dai wannan matakin na da nufin sake duba tsarin kula da harkokin fansho na ritaya da kuma saka haske da gaggawar biyan bukata wajen sarrafa hakkokin masu ritaya wanda sanin a baya aka sha cece-kuce tsakanin wannan hukuma da masu ritaya. Da yake Magana kan wannan batu Chaibou Dambaji, wani jagoran kungiyar Maluman makaranta da ya yi ritaya na ganin an tafka kuskure wajen rushe hukumar ta ‘yan fansho.

Karin Bayani: Nijar: Ko za a biya karin mafi karancin albashi?

Birnin Yamai na Jamhuriyar NijarHoto: Joerg Boethling/IMAGO

Ita dai gwamnati ta sanar da dalilanta na daukar wannan mataki da ya kai ga rusa hukumar wanda suka hada da rashin cin gashin kai na hukumar da ma rashin jami'in lissafin na Asusu hukumar wanda ya haifar da rikici tsakanin babban Daraktan Baitulmalin kasa da Ma'aikatar babban jami'in sarrafa kudi na asusun kasa. Gwamnatin kuma ta nunar da cewa an samu matsaloli na sarrafa hukumar wanda ke haddasa rashin biyan masu ritaya a kan lokaci, ga batun rubanya sunayen masu ritayar da wasu kudaden fansho da ba a biya ba, da kuma batun dakatar da wasu katunan daukan kudi a banki, wanda a cewar Mansour Adamou, daya daga cikin jagororin hadaddiyar kungiyar kwadago ta CDTN,kafin daukar mataki da ya kyautu a sanar da wadanda suka bukaci girka wannan hukuma don jin ta bakinsu:

Karin Bayani: Martani kan karin albashi a Nijar

Tsakiyar birnin Yamai na jamhuriyar NijarHoto: Michael Runkel/imageBROKER/picture alliance

Ko me a ciki dai gwamnati ita ta san inda ruwa ke yi mata yoyo, wanda a cewar Issoufou Boubakar Kado magaji, tsohon babban mai kula da lissafi na asusu gwamnati da yanzu ya yi ritaya sun dade dai suna fashin baki kan wannan batu don a gyara:

Ga lissafin dai wannan hukuma ta ‘yan fansho ta CARENI, ta na bukatar zama ta zamani don inganta tsarin fansho da samar da ingantaccen yanayin rayuwa ga wadanda suka yi ritaya.

Yanzu dai an danka wa ma'aikatar kula da tattalin arziki da kudi ta kasa kula da kudaden ‘yan fansho, wadda ta dauki nauyin biyan dukkannin ‘kudaden yan fansho daga ranar 31 ga watan Disamba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani