1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

130212 Pakistan Regierung

February 13, 2012

Matsaloli da suka haɗa da ƙarancin wutar lantarki da tashin farashin kayayyaki sun daɗe suna ciwa al'ummar tuwo a ƙwarya.

Pakistani Prime Minister Yousaf Raza Gilani attends for a climate debate at the World Economic Forum, WEF, in Davos, Thursday, Jan. 26, 2012. The overarching theme of the meeting, which will take place from Jan. 25 to 29, is "The Great Transformation: Shaping New Models". (AP Photo/Anja Niedringhaus)
Hoto: AP

Wasu masu zanga zanga kenan a Rawalpindi. Suna cewa ku fita Amirka ku fice. Masu zanga zangar 'yan kishin Islama sun yi amannar cewa babu ko tantama babbar matsalar Pakistan ita ce ƙasar Amirka. Majalisar kariya da tsaron Pakistan ita ce sunan da haɗakar ƙungiyoyin addinai suka raɗawa kansu. Su kan haɗu a kai akai a babban taron gangamin magoya baya. Suna ganin ba'a kama hanyar magance muhimman matsalolin da ke addabar ƙasar ta Pakistan ba. Muhimman matsalolin a cewar su guda biyu ne, matsala ta farko ita ce Amirka sannan ta biyun kuma ita ce India.

Hafiz Saeed shugaban ƙungiyar jama'atu Da'awa wadda ake dangantawa da alaƙa da ƙungiyar ta'addanci ta Lashkar Taiba ya fito ƙarara inda yake cewa "Yace yayin da Amirka ke cigaba da kasancewa cikin shiri a Afghanistan domin taimakawa India daga can, da taimakon Allah Mujahidan Taliban a Afghanistan tare da haɗin gwiwa da muslimin Pakistan za su yi maganin wannan kutingwila.

Hoto: dapd

Tun kusan aƙalla shekara guda kenan ake cikin wannan hali, masu kishin Islaman ke fitowa suna magana yayin da su kuwa masu sassaucin ra'ayi basa cewa komai. Ko da yake ala ayya halin bada jimawa masu tsatsauran ra'ayi ka iya zama kan karagar mulki. Bugu da ƙari gwamnatin na fuskantar ƙarin matsin lamba daga jama'a saboda gazawar 'yan siyasar inda ma a yanzu 'yan ƙasar suka dawo daga rakiyar gwamnatin.

Britta Petersen daraktar gidauniyar Heinrich Böll dake birnin Lahore ta ce matsaloli waɗanda suka haɗa da ƙarancin wutar lantarki da tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki sun daɗe suna ciwa al'ummar tuwo a ƙwarya. Ta ce 'yan ƙasar ba jiran samun wani abu da zai fito daga gwamnati, a saboda haka mutum na iya hango yiwuwar tunzuri da bujirewa a irin wannan hali idan mutum ya yanke ƙauna daga jam'iyya ta dimokraɗiyya".

Hoto: picture-alliance/dpa

Britta Petersen ta ce matsalar ma game da makamashi na iya ƙaruwa musamman a lokaci na sanyin hunruru." Ta ce lamarin yana da wuyan sha'ani, hatta a birane kamar Lahore wadda ke da mutane kimanin miliyan takwas a kan sami sao'i takwas zuwa goma babu wutar lantarki ko makamashin Gas. A wasu biranen kuwa lamarin ya fi muni, inda mutane ba za su iya ɗumama ɗakunansu ko kuma yin girki ba".

Matsalar makamashi shine batu ɗaya tilo da fusata al'umar ƙasar. Wannan baɗakala ta sa hatta su kan su sojoji basa sha'awar mulkin domin matsala ce ko ta ina. A cewar wani manazarcin al'amuran siyasa Hasan Rizvi gwamnati na ta kanta ta maida hankali ga matsalolin da suka dabaibaye ta inda ma basa tunanin aiwatar da wasu manufofi da suka shafi rayuwar al'umma.

" Yace matsaloli ne ga su nan kama daga da ɓangaren shari'a da kuma jam'iyun adawa, saboda haka a ko da yaushe suna tunanin ta yaya za su samu su ɗore. Abu na biyu kuma shine rashin ingantaccen tsari da matsalar tattalin arziki wadda basu da mafita sannan kuma ga cin hanci da rashawa da ta yi katutu."

Mawallafi: Kai Küstner / Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh