1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Poland za ta fuskanci kuri’ar amincewa

June 11, 2025

Gwamnatin kasar Poland za ta fuskanci kuri'ar amincewa a majalisar dokoki a wannan Laraba, yayin da take kokarin nuna cewa tana da goyon baya duk da mummunar kaye da ta sha a zaben shugaban kasa.

Firaministan kasar Poland, Donald Tusk
Firaministan kasar Poland, Donald TuskHoto: Pawel Supernak/Avalon/picture alliance

Firaministan kasar Donald Tusk ne ya kira wannan kuri'a bayan nasarar Karol Nawrocki, wani mai ra'ayin kishin kasa, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi cikin wannan watan.

Hakan ya sanya masana yin hasashen cewa gwamnati na iya zama cikin rauni sosai kuma ana iya samun zaben gaggawa.

Nawrocki, wanda ke goyon bayan Shugaban Amurka Donald Trump, ana sa ran zai yi kokarin rushe gwamnatin tare da ƙarfafa jam’iyyar adawa ta PiS wadda ta goyi bayansa.

Donald Tusk, wanda tsohon shugaban kungiyar Tarayyar Turai EU ne ya hau kujerar mulki a shekarar 2023 a matsayin shugaban haɗin gwiwa tsakanin jam'iyyarsa ta masu matsakaicin ra'ayi da jam'iyyar PSL da kuma mai matsanancin ra'ayi.