Gwamnatin Siriya ta fara yunkurin daidaita rikicin kasarta
November 3, 2011![](https://static.dw.com/image/15506847_800.webp)
Kungiyar hadin kan larabawa ta ce gwamnatin Siriya ta amince ta aiwatar da shirinta wanda zai kawo karshen watannin da aka shafe ana zud da jini a kasar. Frime Ministan Katar, Hamad Bin Jassim al Thani, shine ya bada wannan sanarwar lokacin wata hirar da ya yi da manema labarai a birnin Alkahira. Wannan shiri dai ya tanadi gwamnati a damaskus da ta janye dakarunta daga kan tituna, ta kuma sako fursunonin siyasa. Ya kuma hada da baiwa masu sanya ido a kungiyar larabawa da 'yan jarida 'yancin gudanar da ayyukan su a kasar ba tare da matsin lamba ba. To sai dai wasu jami'an diplomasiyya sun nuna shakkunsu suna masu cewa Shugaba Bashar AL-Assad ba zai yi amfani da wannan shiri ba.
Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun ce a tsakanin sao'i 24 da suka wuce yanzu mutane 20 sun mutu.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita : Umaru Aliyu