1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rataye wadanda suka haifar da gobarar daji

Ramatu Garba Baba
October 21, 2021

Gwamnatin Siriya ta tabbatar da zartas da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wasu 'yan kasar 24 da aka samu da laifin haifar da gobarar daji da gangan a yankuna uku na kasar.

Symbolbild Iran Hinrichtung
Hoto: Loredana Sangiuliano/SOPA Images via ZUMA Press Wire/picture alliance

Gwamnatin kasar Siriya ta rataye wasu mutum ashirin da hudu (24) da aka samu da laifin hannu a haddasa gobarar daji da gangan, da ta janyo asarar rayuka da dukiya a cikin kasar a bara. Akwai karin mutum goma sha daya da aka yanke ma hukuncin daurin rai da rai baya ga wasu masu kananan shekaru da aka yanke ma hukuncin zaman gidan yari na shekaru goma da kuma ashirin.

Ma'aikatar shari'ar kasar ta ce, an dai kama mutanen bisa bayanan da aka tattaro, a yayin tuhumarsu sun amince da kunna wutar daji a watannin Satumba da Oktobar bara, baya ga kashe mutane uku, gobarar ta lakume hectocin dubu goma sha uku na gonaki da hectocin filayen noma sama da dubu sha daya baya ga lalata gidaje fiye da dari uku da hamsin. Siriya na daga tsauraran matakai kan masu yi wa kasarta zagon kasa da cin amanar kasa. 

Wannan shi ne karon farko da gwamnati Shugaba Bashar al-Assad ke amincewa da zartas da hukuncin tun bayan da Kungiyar Amnesty International ta soma zargin gwamnatin da yin hakan a bara.