1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Manufofin gwamnatin sojan Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
July 16, 2024

A Jamhuriyar Nijar bayan da Firaministan kasar ya gabatar da alkiblar tsarin gudanar da mulki na shugaban kasa na mulkin soja, tuni aka fara smaun mayar da martani daga 'yan kasa bisa sabbin tsare-tsaren..

Nijar, Yamai | Zanga-zangar goyon bayan sojojin da ke mulki
Magoya bayan sojojin da ke mulki a Jamhuriyar NijarHoto: AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar bayan da Firaministan kasar ya gabatar da alkiblar tsarin gudanar da mulki na shugaban kasa na mulkin Soja Birgediya Janar Abdourahamane Tiani a fannoni daban-daban domin shinfida tsari na gari na tafiyar da mulkin domin al'umma, sai dai kuma wasu na ganin cewa ya kyautu a samar da wannan majalisar tattaunawa da kuma kayyade wa'adin mulki na rikon kwarya a kasar.

Karin Bayani: Nijar: Bukatar sakar wa 'yan siyasa mara

Janar Abdourahamane Tiani shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar NijarHoto: Télé Sahel/AFP

Ita dai wannan kibla ta shugaban kasar na mulkin soja Birgediya Abdourahamane Tiani, ta kumshi manyan digo-digo har guda hudu kama daga batun tsaro, hada kan 'yan kasa, samar da 'yanci na abinci, gudanar da kyakkyawan mulki wanda ake ganin idan hakan ta samu da alama yan kasa za su gani a kasa. Sai dai kuma tuni wasu ke ganin cewa abin da yafi shine na samar da wannan majalisa da aka yi batunta ta tattaunawa da kuma kayyade lokacin mulkin na rikon kwarya daidai da gaskiyar lamarin kasar ta Nijar. Mourtala Abdoul Aziz Nafiou shi ne shugaban kungiyar AJPR ta matasa masu kishin ci gaban Afirka na ganin cewa tsaida wa'adin za sa a zaburar da mutane wajen aiki.

Magoya bayan sojojin da ke mulki a Jamhuriyar NijarHoto: AFP

Sai dai kuma wasu na ganin cewa ai tun farko shugaban kasar ya sanar da aniyarsa ta mika Mulki a wa'adin da bai fice shekaru uku ba, kenan batun majalisar shi ne akasari suke jiran ganin ya wakana. Tuni dai wasu suke ganin cewa duk fa tsarin da za a yi sai 'yan kasa sun hada kai sun mara masa baya idan ana so a cimma buri kuma a cewar Docta Amadou Roufai Lawal batun hadin kai shi ne sahun gaba. A bangare guda Issoufou Boubakar Kado masanin tattalin arziki da gudanar da harkokin mulki ya yi hannunka mai sanda kan mahimmancin yin biyayya ga tsarin tafiyar da ayyuka ta hanyar kaucewa son rai. Tuni dai a wannan tsari na gwamnatin Tiani aka shirya samar da cibiyoyi masu ƙarfi, masu sahihanci da za su daidaita al'amuran jamhuriya ta yadda kowa zai tsaya a matsayinsa ba tare da saka rudani ba ta yadda kowa a matsayin da yake zai san cewa akwai doka kuma tana sama da kowa.