1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ta musanta halaka makiyaya da dama

March 16, 2025

Gwamnatin Burkina Faso ta nuna damuwarta kan labaran da ake yadawa a shafukan sada zumunta na cewa ita ce ta kitsa kashe makiyayan da suka fito daga kabilar fulani.

Wasu makiyaya a yankin Madina Torobe da ke yammacin Afirka
Wasu makiyaya a yankin Madina Torobe da ke yammacin Afirka Hoto: John Wessels/Getty Images/AFP

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta musanta zargin halaka fararen hula, matakin da ya haifar da takaddama da kiraye-kirayen tabbatar da adalci daga kungiyoyin kare hakkin 'dan Adam.

Karin bayani:Human Rights ta bukaci binciken kisan mutane a Burkina Faso 

Gwamnatin gwamnatin mulkin sojin ta ce masu yada wadanda labarai ta kafafen sada zumunta na yin hakan ne domin haifar da rudani a kasar da ke cikin kwanciyar hankali.

Karin bayani: Sabon babi a yaki da ta'addanci a Sahel

Wasu hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna wasu gawarwaki na makiyaya maza da mata da har ma da kananan yara a daddaure. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta HRW ta yi kira ga gwamnatin soja da ke mulki a Burkina Faso, da ta gudanar da cikakken bincike kan wannan mummunan kisan gilla da aka yi wa gomman fararen hula a yankin Solenzo na yammacin kasar.