Gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar soja da Amurka
March 17, 2024Sanarwar katse huldar sojan tsakanin Nijar da Amurka na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da wata tawagar Amurkawa da ta ziyarci Nijar ta gaza yin tozali da shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdourahamane Tiani.
A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar ceton kasar ta Nijar (CNSP) ya karanta a gidan talabijin mallakar gwamnati, Amadou Abdramane ya bayyana cewa sojojin na Amurka na jibge ne a Nijar ba bisa ka'ida ba, kana kuma hakan ya saba wa ka'idoji da dokokin kundin tsarin mulkin kasar da ke yankin Sahel.
Kazalika ya kuma yi Allah wadai da zargin nuna isa da shugabar tawagar Amurkawan Mme Phee ta nuna a lokacin ziyarar kwanaki uku da suka kai Nijar a farkon wannan mako, abin da ya kira da yunkurin lalata huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
Kimanin sojojin Amurka 1,100 ne ke girke a Nijar domin yakar kungiyoyin jihadi baya ga kuma wani babban sansani na jirage marasa matuka a jihar Agadez da ke arewacin kasar.
Karin bayani: Amurka za ta mayar da sojojinta Agadez
Bayan korar sojojin Faransa, wannan yunkuri na raba gari da Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin na Nijar ke karfafa hulda da wasu kasashe inda Rasha da Iran ke a sahun gaba.