Gwamnatin Sokoto ta soke izinin mallakar gidaje
August 29, 2025
Gwamnatin jihar Sokoto ta soke duk wasu takardun mallakar gidaje ko fili ko gonaki a jihar tun daga lokacin da aka kirkiri jihar zuwa yau, shekaru 50 ko fiye da suka gabata. An bai wa al'ummar wa'adin watanni 4 domin sabunta takardun nasu. Sai dai wasu na ganin yunkuri ne na kuntatawa duba da halin da ake ciki na matsaloli irin na tattalin arziki da tsaro.
Sabuwar dokar da gwamnatin jihar ta Sokoto ta bullo da ita na fuskantar sharhi da ma fassara a tsakanin al'ummar jihar dangane da inda ta sa gaba. Malam Buhari Namalam ya yi nazarin abin da gundarin dokar ya kunsa.
''Takardar mallakar wuri, gwamnati kadai ke iya saka mata hannu kuma za ta iya baka damar amsar bashin banki domin kowa yasangwamnatita mallakamaka wannan gidan.''
Da alama dai wannan matakin ya jefa rudani a zukatan mamallaka gidaje a jihar irin su Malam Mainasara Ladan.
Da yake dokar ta shafi wadanda suka taba mallakar takardun na mallakar gidaje ne, sai dai a cewar Malam Aminu Gandhi wani dan kasuwa mai gudanar da harkokin masana'antu tabbas wannan doka ka iya kawo nakasu ga masu yunkurin kafa masana'antu da saka hannun jari.
"Abin da ka iya kawo wa dokar matsala shine kudin da aka saka, duba da irin halin da ake ciki.”
A cewar Barista Safiya Ahmed Usman wadanda abin ya shafa na da damar tunkarar kuliya ne kawai yayin da gwamnatin ta fara masu kaddarori.
"Akwai dokar amfani da gidaje wadda ta saka komai hannun gwamna, sai dai wadanda abin ya shafa za su je kotu.”
Tuni dai wasu da abin ya shafa suka garzaya kotu domin kalubalentar wannan mataki na gwamnatin jihar ta Sokoto.