Sudan ta cimma yarjejeniya da Isra'ila
October 23, 2020Isra'ila da Sudan sun amince su dawo da hulda a tsakaninsu. An dai cimma wannan matsaya a sakamakon shiga tsakani da Amirka ta yi a wannan Juma'a. Shugaba Donald Trump ya kasance a zaman da aka yi ta wayar da tarho da Firai Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da takwaransa na Sudan Abdallah Hamdok a kulla yarjejeniyar.
Kasashen biyu sun cimma matsaya kan batun inganta tattalin arziki inda suka amince su soma da bude kafar hada-hadar kasuwanci a tsakaninsu. Cikin watan jiya ne Kasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, suka dawo da dangantaka tsakaninsu da Isra'ila.
Daman shugaban na Amirka ya ce wani sharadin soke sunan Sudan daga jerin kasashen, shi ne ta amince da dawo da hulda da Isra'ila tare da biyan diyya ga wasu Amirkawa da hare-haren ta'addanci ya rutsa da su a shekara ta 1998 a Sudan.