Gwamnonin APC na son Buhari ya zarce
February 23, 2018Matakin gwamnonin dai na zuwa ne lokacin da wasu 'yan majalisar dattawa da wasu tsoffin gwamnoni ke adawa da yunkurin zarcewar shugaba Buharin, sai dai daga dukkan alamu bakin alkalami ya bushe kan batun sake takarar shugaban kasar bayan taron gwamnonin jam’iyyarsa ta APC ya bayyana bukatar son sake takarar shugaban a zabe a 2019.
Duk da cewa gwamnonin basu bada tabbacin amsa bukatarsu daga shugaban kasar ba, amma gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha kuma shugabn kungiyar gwamnonin APC ya ce " Muna dab da su shawo kan shugaba Buhari, domin cika burinmu na sake tsayawa jam’iyyar APC takarar shugabancin Najeriya. Ya ce mana sai nan gaba zai ba mu amsa ko zai tsaya ko bai zai tsaya ba, amma dai muna ganin alamu zai yarda da bukatunmu."
Kokari na sauyi ga kasa ko kuma kokari na fakewa a cikin inuwa ta shugaban kasar, ana kallon matakin gwamnonin a matsayin wani kokari na bada kariya ga shugaban kasar da ya dauki lokaci yana shan suka daga sassan kasar daban daban.
Sannu a hankali dai majalisar dattawan ta rikide ya zuwa dandali na masu adawa da shugaban kasar, sakamakon rikicin dake tsakanin gwamnonin da 'yan uwansu dattawa a majalisa. Rikicin da kuma da a halin yanzu ya rikide ya zuwa rikicin manya a cikin APC, sannan kuma ya bazu zuwa rassan jihohi daban daban.
Rikicin baya-bayannan dai shi ne takun saka tsakanin wasu sanatoci da gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasiru El-Rufa'i, inda wasu bangare na jam'iyar suka sanar da korar gwamnan abinda ya haddasa rusa sakatariyar jam'iyyar APC da ke jihar Kaduna. A makon gobe ne dai aka tsara babban taron jam’iyyar APC na kasa, da nufin nazarin jerin rigingimun dake fuskantar jam’iyyar a yayin da zabukan kasar ke kara karatowa.