1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Gwarzon Barcelona Lamine Yamal zai yi jinyar makonni

October 4, 2025

Mai horas da kungiyar Barcelona Hansi Flick ya ce babu ranar da dan wasan kungiyar Lamine Yamal zai dawo taka leda.

Lamine Yamal na FC Barcelona a wajen bikin Ballon d'Or na 2025
Lamine Yamal na FC Barcelona a wajen bikin Ballon d'Or na 2025 Hoto: Benoit Tessier/REUTERS

Wasu kafafen yada labaran Spain sun rawaito cewa Yamal zai shafe makonni uku yana jinya sakamakon rauni da ya samu a makarfafa, yayinda Flick ya ce akwai yiwuwar ya zarta hakan.

Karin bayani: 'Dan wasan Spain Lamine Yamal ya kafa tarihi a gasar Euro

Gwarzon dan wasan na Spain ba zai samu damar buga wasan shiga gasar cin kofin duniya ba, duk da cewa ana hasashen cewa zai iya dawowa a fafatawar da Barcelona zata yi da Real Madrid a ranar 28 ga watan Oktoba.

Karin bayani: Shin wane ne zai lashe kyautar Ballon d'Or

Yamal wanda ya zo na biyu a bikin gasar karbar lambar yabo ta Ballon d'Or ya samu rauni ne lokacin da Barcelona ke fafatawa da Paris Saint-Germain a gasar Champions League a watan Satumba.