Najeriya: Gyara sashin shari'a domin kwatanta adalci
April 29, 2024Tafiyar hawainiyar da sashin shari'ar Najeriyar ya dade yana yi abinda ke shafar yadda ake gudanar da kotuna da ma shari'ar kanta da ke tafiya a karkace ya sanya wannan kiraye –kirayen. Domin karfin fada a ji da alkalin alkalai na Najeriya ke da shi a sashin shari'ar kasar ya sanya shi zama mai cikakken iko a kan gudanar da daukacin al'ammuran wannan sashi da ke da muhimmancin gaske ga tsarin dimukuradiyya.
Kokari na ganin tasirin wadanan sauye-sauye muhimmi ne ga sashin sharai'ar na Najeriya da ya dade yana fuskantar zarge zarge a fanin aiwatar da hukunci saboda matsaloli na cin hanci da rashawa. Barrister Mainasawa Umar masani a fanin shari'a a Najeriya na mai cewa somin tabi ne batun rage karfin alkalan alkalan in har ana son ganin tasirin lamari sai an aiwatar da cikakken garambawul ga sashin shari'ar Najeriyar.
Duk da masdu raji na gudanar da wadannan sauye-sauye a sashin shari'ar Najeriyar aiki na gaban majalisar dokokin Najeriyar da ke aikin gyaran fuska ga tsarin mulkin kasar da mafi yawan alummar kasar ke koken na bukatara a yi masa wankan tdsarki don dacewa da bukatu da muradun alummar kasar.