1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gyaran dokar zabe zai taimaki siyasa?

Uwais Abubakar Idris
May 8, 2026

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da gyaran fuskar da aka yi wa dokar zabe ta 2026, wanda zai hana kai kararraki barkatai a kotuna da dama kan korafi guda daya da ya shafi zaben fidda gwani.

Najeriya | Siyasa | Zabe
Amincewar da majalisar dokokin Najeriya ta yi da dokar zabe zai taimaka?Hoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

Majalisar dattawan Najeriyar ta dauki wannan matakin ne, domin toshe kafar da 'yan siyasa ke amfani da ita wajen haifar da rudani ta hanyar amfani da kotuna. An yi gyaran fuska ga sashe na 28 na dokar zabe Najeriyar ta 2026, biyo bayan sabanin da ake samu a kan kotun da ke da hurumin sauraren kararrakin zaben fidda gwani. Wannan lamari dai, tuni yake tayar da jijiyar wuya da kama hanyar jefa dimukurdiyyar Najeriya cikin halin rudani.

Rudani da rashin tabbas a siyasa

Wannan ya haifar da tsoron barin kotuna su jefa dimukurdiyyar cikin halin lalube da rashin tabbas. Halin da ake ciki na rigigimun fitar da 'yan takara da ke faruwa musamman a jamiyyar APC mai mulki, inda a jihohi fiye da 10 ake fuskantar takaddama a kan matakin da gwamnaonin suka dauka na nada wanda suke son ya gaje su maimakon zaben fitar da gwani ya sanya wannan dokar da majalisar ta amince da ita ta zo a kan gaba. A yanzu sabuwar dokar da majalisar ta amince da ita, ta samar da dokar da ta taka birki ga kotunan Najeriya.

Kalubalen da ke gaban hadakar ADC a babban zaben Najeriya

44:35

This browser does not support the video element.

Kowace kotu ta san cewa, tana da iyakar huruminta na kararrakin zaben fitar da gwanin da za a yi. A bisa tanadin dokar da aka amince da ita, za a fara kararrakin da suka shafi zaben fitar da gwani na 'yan majalisun dokikin jihohi da na tarayya da gwamnoni a kotunan tarayya zuwa kotun daukaka kara. Yayin da na zaben fitar da gwani na shugaban Najeriya za a fara daga kotun daukaka kara zuwa kotun koli.

Kotunan Najeriya sun zama 'yan amshin shata?

A 'yan watanin baya-bayan nan dai, ana nuna damuwa a kan yadda kotunan suka zama wani dandali da 'yan siyasa ke amfani da shi domin biyan bukatun kansu ba wai neman a yi musu adalci ba. Wannan lamari na haifara da rudani ga tsarin siyasar Najeriyar da ka iya shafar tsarin dimukurdiyyar kasar kansa, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar babban zabe.

 

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani