Shirin gyaran bangaren shari'ar Nijar
February 2, 2023Tsarin zai kuma shafi tsarin gurfanar da masu laifi a gidajen yari ganin yadda gidajen yari suka cika suka batse a kasar ta Nijar. Kasar Holland da yanzu haka wasu ministocinta biyu ke ziyara a kasar ta Nijar, ta sha alwashin kama wa sashen na shari'a domin cimma wannan buri a kasar ta Nijar.
Wannan katafaren tsari dai za a iya cewa zai kawo manyan sauye-sauye ga al"amura na yau da kullum da ma ci gaban kasar ta Nijar domin idan akwai tsari da kiyaye harkokin shari'a ta hanyar hukunta masu laifi daidai da laifinsu to za"a samu ci gaba a fannoni da dama. Da yake magana kan wannan batu ministan shari'a na jamhuriyar Nijar Ikta Abdoulaye Mohamed, ya nuna gamsuwar shi ga manyan tsare-tsare da kasar ta runguma a fannin shari'a tare da kasasashe da kungiyoyi da ke dafawa.
"Muna aiki ne da wani tsari na inganta harkokin fannin shari'a wanda ya shafi mutane da ke bukatar tallafi na gaggawa a fannin shari'a, kuma masu cin moriyar tsarin su ne manyan ma'aikatu da ma'aikatansu ta yadda za a rinka rigakafin duk wasu matsaloli na fannin shari'a. Tsari na biyu muna yin shi ne da kungiyar Idlo ta kasa da kasa mai kula da fannoni na shari'a, inda muke kokarin karfafa mashara'antunmu daban-daban na jihohi. Wannan tsari kuma na aiki da fannin manyan laifuka a mashara'antu na Dosso da Tahoua da Tillabery, kuma nan gaba zai shafi babbar mashara'anta ta birnin Yamai".
Katafaran tsarin da ma'aikatar shari'a ta jkasar ta Nijar ke samarwa sannu a hankali ya samu goyon bayan kasashe irin su Nedeland wanda wata babbar tawaga da ministoci biyu suke jagoranta ciki har da ministar kula da harkokin kasuwanci da huldar kasa da kasa wadda ta yaba tsarin na Nijar a fannin inganta harkokin shari'a.
"A yau zamu iya ci gaba da tattaunawar da muke ta karfafa hulda ta tsakanin kasa da kasa a fannin shari'a, kuma na yi farin ciki da kuka ambato wasu daga cikin tsare-tsare da muke yi tare a fannin tsaro da mulki na doka wanda shi ne tsari mai mahimmanci wanda muka tattauna a kai lokacin da ministan shari'a na Nijar ya kawo ziyara a kasar Holand. Domin abun da al'umma take bukata ita ce shari'a kuma nasan muna da ra'ayi guda kan haka domin ta haka ne ake samun cudanya tsakanin al'umma da riga kafin duk wani rikici da kuma samun zaman lafiya mai dorewa. "
A kokarin da hukumomin na shari'a ke yi a Nijar na inganta wannan fanni, tuni dai ake daf da magance dadewar masu manyan laifuka a gidajen yari ba tare da shari'a ba wanda yanzu yanna lamari ya sauya tare da taimakon kungiyar nan ta Idlo a cewar mai shari'a Mamane Sani Ousseini Jibaje babban jami'i a ofishin ministan shari'a ta kasar Nijar.
Abun jira a gani dai shi tasirin da wadannan tsare-tsare za su yi a fannin shari'a a kasar ta Nijar, ta yadda al'umma za ta ci gaba da nuna yarda da mashara'anta da kuma yadda mashara'anta za ta zama garkuwa wajen kare hakkokin jama'a da inganta incin dan Adam ba tare da wani katsalandan na yan siyasa ba.