1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗewar ƙungiyoyin 'yan tawayen Siriya

November 11, 2012

Ƙungiyoyin 'yan tawayen Siriya sun cimma yarjejeniya ta amincewa da su haɗe waje guda domin cigaba da fafutukar su wajen ganin bayan mulkin Shugaba Bashar al-Assad.

Hoto: KARIM JAAFAR/AFP/Getty Images

Dazun nan ne a birnin Doha na daular Qatar ƙungiyoyin su ka ce sun sanya hannu kan yarjejeniyar da nufin kaiwa ga curewa waje guda bayan da su shafe kwanaki su na gudanar da tattaunawa, biyo bayan matsin lambar da su ka yi ta sha daga ƙungiyar ƙasahen larabawa da kuma Amurka na su kasance tsintsiya maɗauriki ɗaya a fafutukar da su ke.

Da ya ke magana da manema labarai bayan amincewa su girka ƙungiya ɗaya tilo ta 'yan tawayen na Siriya, Sadr Iddine al-Bayanouni da ke zaman ɗaya daga cikin fitattun masu adawa da Assad ya ce duk da cewar sun yi ta kai ruwa rana da 'yan uwansu, yanzu haka sun amince da su kasance ƙarƙashin inuwa guda.

Yayin da 'yan tawayen na Siriya ke ƙoƙarin haɗewa, a hannu guda kuma dazun nan Isra'ila ta ce ta yi harbe-harbe cikin ƙasar ta Siriya a wani mataki na tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro, bayan aka harba rokoki tuddan nan na Golan wanda ƙasar ta Bani Yahudu ke mamaye da su. Masu sanya idanu kan rikicin na Siriya dai na ganin mataki na Isra'ila ka iya dagula halin da ake ciki a Siriyan.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Ahmed Salisu