Ana yunkurin shawo kan rikicin Habasha da Tigray
November 9, 2020A cikin wata sanarwar Firaminista Abiy Ahmed na kasar Habasha, ya nada Janar Birhanu Jula a matsayin babban hafsan sojojin kasar domin maye gurbin Janar Adem Mohammed wanda babu wanda ya san matsayin da zai kasance bayan tunbuke shi daga mukamin. Sabon babban habsan sojan, Janar Jula ya karbi aikin tafiyar da rundunar sojan yayin da ake kara samun yawan sojojin da suka jikkata bayan kwashe kwanaki ana fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da 'yan awaren yankin Tigray na arewacin kasar.
Bangaren gwamnati dana 'yan tawaye na zargin juna
Yan awaren na TPLF da ke rike da madafun iko a yankin na arewacin Habasha, wadanda gwamnatin kasar ke zargin neman kawo turmutsi domin jefa kasar cikin rudani da rashin iya tafiyar da harkokin yau da kullum. A daya bangaren jagororin yankin na Tigray sun zargi gwamnatin Habasha da gazawa da kuma zargin cin hanci da rashawa a yayin da gwamnatin ke kawar da kai ga abin da saura ke aikatawa.
MDD ta damu da rayuwar fararen hula
Firaiminista Abiy Ahmed ya kaddamar da sabbin hare-hare ta sama kimanin 10 kan 'yan awaren wanda yake zargin sun yi abin da za su yi domin karya kundin tsarin mulkin kasar ta hanyoyin da dama inda a jawabinsa ya kara da cewa..."Lokacin aka dage zaben kasa da aka tsara a wannan shekar zuwa shekara ta 2021 saboda annobar Covid-19 ta hanyar da kundin tsarin mulki ya amince da yardar majalisar dokoki ta Tarayya, sai 'yan TPLF suka saba kundin tsarin mulkin, suka gudanar da zaben da ya karya ka'ida inda ta lashe daukacin kujerun majalisar dokokin yankin." Tuni Majlaisar Dinkin Duniya ta bukaci duk bangarori, da su guji jefa kasar cikin yanayi na rudani, ta kuma nemi a bayar da damar kyale ma'aikatan jinkai don gudanar da aiyukan isar da agaji ga wadanda ke da bukatar taimako, tare da gargadin cewa ana iya shiga mawuyacin halin jinkai idan ba a mutunta umarnin ba.