WHO ta nuna damuwa kan yankin Tigray
November 12, 2021Talla
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniyar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna damuwar tasa ne tare da yin gargadin cewa al'ummar yankin na cikin halin matsananciyar yunwa da ka iya halaka su, baya ga wadanda ke mutuwa sakamakon rashin magunguna. Ghebreyesus da shi ma ya fito daga yankin arewacin Tigray din, ya yi wannan gargdin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishin hukumar ta WHO da ke Geneva. A cewarsa hukumar ba za ta iya tura kayan agaji zuwa yankin na Tigray ba, sakamakon yadda aka killace yankin baki daya. Firaminista Abiy Ahmed na Habasha, ya kwashe tsawon shekara guda yana fafata yaki da mayakan yankin na Tigray, wadanda a yanzu haka suke kokarin isa Adis Ababa babban birnin kasar.