Habasha: Halin da ake ciki a Tigray
November 9, 2020Talla
Majalisar Dinkin Duniya tare da wasu hukumomin sun baiyana damuwa kan dokar hana zirga-zirga da Firai minista Ahmed ya kakaba a makon da ya gabata ya kuma tura jami'an soji zuwa yankin arewacin kasar don kawo karshen wani boren 'yan tawaye da ake zargin jami'iyya mai mulki ta Tigray People's Liberation Front ta yi.
Sai dai sakamakon katsewar internet da layukan waya da aka toshe ya haifarwa 'yan jarida a Adis Ababa kasa fahimtar abin da ake ciki a Tigray da ke da iyaka da Eritrea.
Firai minista Ahmed ya jaddada damuwarsa na fadawar kasar Habasha cikin rikici a shafinsa na Tweeter. Ka zalika ana ganin cewar martabar Abiy da a bara aka bashi lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ka iya zubewa idan kasar ta shiga mummunan yakin basasa.