1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Al'aduAfirka

Habasha : Shekaru 40 da kafa gidauniyar yaki da yunwa

Abdourahamane Hassane
November 25, 2024

An cika shekaru 40 da taurarin mawakan Burtaniya da Irland suka raira waka mai taken "Do They Know It's Christmas" domin tattara kudade don taimaka wa wadanda yunwa ta shafa a kasar Habasha a shekarar 1984

Band Aid 2024 | 40-jähriges Jubiläum mit neuer Version von "Do They Know It's Christmas?"
Hoto: Brian Aris/Band Aid/PA Wire/picture alliance

 A shekara ta 1984, kasar Habasha da ke a gabashin Afirka ta fuskanci mummunan fari wanda ya lalata yawancin amfanin gona. Kusan mutane miliyan takwas ne yunwa ta shafa; Hotunan mutanen da ke fama da yunwa, musamman na yara, sun zagaya cikin duniya kuma sun haifar da shirin ba da gudunmawar da ba a taɓa gani ba.

Mawakin Burtaniya Bob Geldof, nan take ya yanke shawarar daukar mataki tare da abokinsa mawaƙin Midge Ure, sannan ya tara ƙungiyar taurari don samar da waƙar. An fara hada wakar a ranar 25 ga watan Nuwamba, na shekara ta 1984

Mawakin Burtaniya Bob GeldorfHoto: picture alliance/Avalon

Taurari na Birtaniya da Irland wadanda suka hada da Paul Young, da Boy George, da George Michael, da Phil Collins, da Annie Lennox, da Duran Duran, sun raira wakar ta  Do They Know It's Christmas don samar da kudaden taimaka wa Habasha

Hakan ya harzuka taurari Harry Belafonte wanda ya ga dukkanin wadanda suka yi wakar Turawa ne da nufin tamaka wa Afirka, shi ya sa ya ce mai zai hana sauran mawaka bakar fata su kawo tasu gudunmawa.

Gangamin mawaka a LondonHoto: picture-alliance/dpa/N. Försterling

A kan haka Harry Belanfonte ya samu irin tunani na Bob Geldof, ya tuntubi mawaka irinsu Lionel Richie, da  Michael Jakson domin kirkirar wakar da ake kira da suna  "We Are The World"

 Taurari irinsu Stevie Wonder, da Bob Dylan, Tina Turner, Cyndi Lauper, Al Jarreau, Diana Ross, dukkaninsu suna daga cikin mawaka 20  wadanda suka raira wakar da ta samu karbuwa a duniya wacce aka fitar da faifaye miliyan 20 wadanda akanta aka tattara kudade kusan bilyan 63 na dala Amurka domin taimaka wa Habasha a shekarar 1985

Gangamin mawaka a LondonHoto: Fox Photos/Hulton Archive/Getty Images

Sai dai duk da sha'awar ayyukan agajin da mawakan suka yi an rika yin suka musamman a kan waka ta farko, "Do They Know It's Christmas"  "Shin sun san Kirsimeti ne?".

 Ana ganin ba daidai ba ne a ɗauka cewa mutanen Habasha, waɗanda suke cikin al'ada a cikin tsofaffin Kiristoci a duniya, ba su san cewa Kirsimeti ne ba,

Masu yin sharhi a kan al'amura, na ganin wannan wulakanci ne kuma yana nuna karara ra'ayin 'yan mulkin mallaka na yammacin duniya a kan Afirka.

An ci gaba da sukar wakar a tsawon shekaru da sigarta da aka sake a shekara ta 2004 tare da Paul McCartney, da Robbie Williams da Dido, da kuma a shekara ta 2014 lokacin da Bob Geldof ya sake hada mawaka don tara kudade ga wadanda cutar ta Ebola ta kama.