1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHabasha

Yaki ya yi muni a yankin Amhara

Ololade Adewuyi ZU
August 16, 2023

Wani sabon tashin hankali na ci gaba da ruruwa a yankin Amhara na kasar Habasha. Hakan ta biyo bayan rikicin da ya kaure a tsakanin sojojin gwamnati da mayakan da ke tsaron yankin.

Sojojin Habasha
Sojojin HabashaHoto: Ethiopian News Agency/AP/picture alliance

Wannan rikici dai ba shi da alaka da wanda ya faru a yankin Tigray shekaru biyu da suka wuce a Habasha. Sabuwar fitinar da ta kunno kai a yankin Amhara da ke makwabtaka da yankin na Tigray ta yi sauki a ranar Talatar da ta gabata bayan da sojojin gwamnatin Habasha suka yi wata mummmunar artabu a tsakaninsu da mayakan yankin Amhara da ake wa lakabi da Fano. Kafin lafawar da kura ta yi a baya-bayan nan, mutane 26 ne suka rasa rayukansu a gumurzun da bangarorin biyu suka yi. Ana zargin gwamnati ce ta fara takalar fada ta hanyar kai wa mayakan yankin hari ta sama, lamarin da ya fusata mayakan na Fano daukar makamai domin su fafata da dakarun gwamnati. Domin shawo kan sabon rikicin, majalisar dokokin kasar ta yi gaggawar amincewa da kakaba dokar ta baci a yankin na Amhara gaba daya kamar yadda dan majalisa Tesfaye Beljige  ya yi karin haske:'' Zaman lafiya da batutuwan da suka shafi tsaro abubuwa ne da tsarin mulkinmu bai dauka da wasa ba, za su iya taba kimar kasarmu tare da dagula mana zaman lumana. Domin dakatar da hakan, dokar ta bacin da muka sanya ta zama wajibi. Beljige ya kuma zargi mayakan sa-kai na yankin Amhara da janyo wa yankinsu rikicin da ke neman jefa mutanen yankin cikin halin ha-u-la'i: ''Tayar da kayar baya ba bisa ka'ida ba da mahukunta a yankin Amhara suke yi na haifar da barazanar tagayyara jama'a da lalata dukiya gami da kisa tare da jefa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba cikin wahala. A takaice dai wannan abu da suke yi ya samar da barazana ga mazauna yankin.''

Masu fafutuka kare hakkin dan Adam na nuna damuwa a kan yaki

Sojojin HabashaHoto: Ethiopian News Agency/AP/picture alliance

Rincabewa da rikidewar da wannan rikici na Amhara ke kokarin yi ne suka sanya masu fafutukar kare hakkin dan Adam a yankin nuna damuwa kan taho-mu-gamar da aka yi, suna masu Allah wadai da kamen  da dakarun gwamnati ke yi wa mutane 'yan kabilar Amhara. Gedu Andargachew na cikin tsofaffin shugabannin yankin na Amhara, ya kuma yi gargadin amfani da karfin bindiga wajen shawo kan matsalar: ''Idan har ana muradin magance wannan rikici cikin adalci babu yadda za a yi amfani da karfin soji kamar yadda aka yi a wani yankin na kasar. Tattaunawa ita ce mafita.'' Rikicin yankin na Amhara ya fara kunno kai ne tun bayan da gwamnatin Habasha ta yanke shawarar cusa mayakan yankin a cikin rundunar soji da 'yan sanda ba tare da sahalewar mutanen yankin ba. Hakan kuma na zuwa ne watanni bakwai bayan kawo karshen rikicin yankin Tigray da ya yi shekaru biyu yana lakume rayuka tare da tagayyara jama'a a wannan kasa ta Habasha da ke zama kasa ta biyu mafi yawan mutane a nahiyar Afirka.