1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha ta taka rawar gani a fannin kula da lafiyar kananan yara

September 25, 2013

Majalisar Dinkin Duniya ta yaba wa Habasha bisa matakan da ta dauka na dakile mutuwar yara 'yan kasa da shekaru biyar.

Ethiopian state television announced on August 21, 2012 that Hailemariam Desalegn will be acting prime minister, after the death of Ethiopian Prime Minister Meles Zenawi.
Hoto: CC-BY-SA- World Economic Forum

A dai dai lokacin da babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York na Amirka ke tattauna muradun karni, Habasha ta shiga cikin jerin ƙasashen da suka samu ci gaba ta fannin raguwar mace macen kananan yara, kamar yadda hukumar kula da muradun ci gaban ƙarni ta Majalisar Dinkin Duniya wato MDG a takaice ta bayyana. A rahoton da ta fitar, hukumar ta ce wasu ƙasashen, sun cimma wannan burin, shekaru biyu gabanin wa'adin da aka tsayar na magance mace-macen yara 'yan ƙasa da shekaru biyar.

Ƙasar ta Habasha dai ta samu raguwar yara 'yan shekaru biyar da haihuwa wandanda ke mutuwa da kashi biyu cikin uku, a cikin shekaru 20 da suka gabata. Hakan yana nufin daga yara 1,000. dake mutuwa, a yanzu yayi ƙasa da yara 68 ne ke mutuwa. Shanta Boemen ita ce mai magana da yawun asusun kula da yara ƙanana na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF a ƙasashen kudu da Sahara:

Ta ce "Hakan yana nufin ana ceton rayuka kimanin yara dubu 200 a ko wace shekara a ƙasar Habasha kawai. Wannan abu, yana da matuƙar tasiri."

Hoto: AP Photo

Salon yaki da mutuwar yara a Habasha

Wannan lamarin yana nufin ƙasar Habasha ba ƙaramin mataki ta dauka ba, don haka asusun UNICEF ke cewa, a ƙasar an ƙaddamar da juyin juya hali kan batun da ya shafi kiwon lafiya, musamman a ka fifita wani ɓangare a kiwon lafiya.

Ta ce "Gwamnatin ta zuba jari mai yawa a fannin kiwon lafiya daga tushe. Wannan kuma shi ne sakamkon tsayin daka da akayi"

Gwamnatin ƙasar ta Habasha dai ta maida hankali ne kan kula da lafiyar jama'a a karkara. Shekara ta 2003, ƙasar ta fara wani shiri na bada himmma ga kiwon lafiya a ko wane lungu da saƙo, inda mutanen karkara da a da basu da daman ganin likita, a yanzu sai gashi su ne gwamnati ta tashi haiƙan don kula da lafiyarsu. Hakan kuwa yasa ƙasar Habasha ta kasance ita ce ƙasar Afirka ta farko da ta fara zuba jari kan kiwon lafiya a karkara.

Sakatare janan na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moonHoto: Getty Images

Darasi ga sauran kasashen Afirka

Hakan dai yana nufin bada horo ga jami'an kiwon lafiya kimanin dubu 38 a ko wace shekara guda. Ba wai wannnan lamari ne na gaggawa ba, an baiwa jami'an kiwon lafiya a karkara horo mai zurfi. Kuma an bada mahimmanci wajen tabbatar da biyansu albashi. Domin bai wa ma'aikatan ƙwarin gwiwa ta yadda za su yi aiki bil-haƙƙi bisa horon da suka samu"

A shirin da gwamnatin Habasha ta ƙaddamar dai, an tabbatar da cewar, dole a samu ma'aikatan kiwon lafiya a ko wace ruga, wadanda kuma ke da horon iya kula da kiwon lafiyar jama'ar rugagen, tare da isassun magunguna kan cututtukan da suka fi damun yara ƙanana a ƙasar Habasha. Akarin cututtukan da suka fi hallaka yara a ƙasar su ne, zuyoyi da kuma cutar huhu, da zazzabin cizon sauro.

Masu kiwon lafiya kuma suna fadakar da jama'a, da su rinka kwana cikin gidan sauro.

Yanzu haka dai wasu ƙasashen Afirka sun fara yin koyi da ƙasar ta Habasha a fannin kiwon lafiya.

Mawallafi : Rühl, Bettina / Usman Shehu Usman
Edita : Saleh Umar Saleh