1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kai hari kan makarantar yara

Ramatu Garba Baba
August 27, 2022

Yara na daga cikin wadanda suka mutu bayan wasu hare-hare ta sama da ake zargin rundunar sojin Habasha da kai wa kan wata makaranta renon yara.

Tigray-Krise in Äthiopien
Hoto: UGC/AP/picture alliance

Yara kanana na daga cikin mutum hudu da suka rasa rayukansu a wasu hare-hare ta sama da ake zargin sojojin Habasha da kai wa a kan wata makarantar renon yara da ke Makele na yankin Tigray. Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya tabbatar da labarin harin inda ya yi Allah-wadai da yadda rikicin ke shafar yara kanana. 

Rikici a tsakanin gwamnatin Habasha da Tigray, ya  jefa miliyoyi da ke a yankin na Tigray cikin halin kunci na katsewar abubuwan more rayuwa inda aikin isar da agaji ke ci gaba da fuskantar tsaiko.