1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Gargdin Ellon Musk kan zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 3, 2025

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Robert Habeck ya gargadi babban mai kudin Amurka Elon Musk da kada ya kuskura ya yi shiga sharo ba shanu a zaben kasar da ke tafe.

Jamus | Robert Habeck
Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Robert HabeckHoto: Kira Hofmann/photothek.de/picture alliance

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Robert Habeck ya yi wannan gargadin ne a wata hira da ya yi da Mujallar Spiegel, bayan da aka tambaye shi ko Musk na zaman barazana ga kasarsa a zaben watan Fabarairu mai kamawa. Musk da ya yi fice wajen yin rubutun tunzuri a shafinsa na X ya jima yana tayar da zaune tsaye a siyasar Jamus, inda a karshen makon da ya gabata ya ayyana goyon bayansa karara ga jam'iyyar AfD mai tsananin kishin kasa da kyamar baki a zaben kafin wa'adi da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairun da ke tafe a Jamus din.