Coronavirus za ta kawo karshe da hadin kai
December 22, 2021Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce dole a tanadi yawan allurar-rigakafin cutar corona da za su wadata duniya kafin a yi tunanin iya dakile annobar daga doron kasa.
A cewar shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce, rige-rigen da manyan kasashen duniya ke yi na son ganin mutanensu sun yi akalla rigakafin uku ba zai taba yin wani tasiri a hana yaduwar cutar ba muddun ba a yi raba a tsakanin kasashe masu shi da babu ba. Ya kara da yin gargadi ga masu ganin, sun yi allurar za su iya watayawa a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara da ke tafe ba tare da sun kamu da cutar ba.
Masana kimiya dai, na ci gaba da nuna fargabar yaduwar sabon nau'in Omicron da ake ganin na da hadari a lokacin bukukuwan al'amarin da suka ce, ka iya mayar da hannun agogo baya a yaki da cutar da ta addabi duniya.