1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hadin kai kan yaki da ta'addanci

Suleiman Babayo MA
June 24, 2024

Shugaban Mauritaniya ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen Afirka ta Yamma domin yaki kungiyoyin masu ikirarin jihadi, yayin da shugaban yake yakin neman samun wa'adi na biyu na shugabancin kasar.

Shugaba Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani na Mauritaniya ya nemi ganin hadin kai tsakanin kasashen Afirka ta Yamma domin yaki kungiyoyin masu ikirarin jihadi. Shugaban ya fadi haka lokacin hira da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, gabanin zaben shugaban kasar da za a gudanar a karshen mako da muke ciki.

Shi dai Shugaba Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani mai shekaru 67 tsohon hafsan soja kana tsohon ministan tsaro, yana neman wa'adi na biyu na mulki, inda yake karfafa batun tsaro a kasar mai yawan mutane kimanin milyan hudu da rabi.