1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An sake kaiwa Hadaddiyar Daular Larabawa

Binta Aliyu Zurmi
January 24, 2022

Ma'aikatar tsaro ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da yin nasarar dakile wasu jerin hare-hare har guda biyu na makamai masu linzami da ke cin dogon zango da mayakan Huthi suka harba musu.

Abu Dhabi Flughafen
Hoto: KARIM SAHIB/AFP

Makaman da aka harba zuwa birnin Abu Dhabi sun sauka ne ba tare da jimma kowa da ma yin ta'adi ba. A sanarwar ta wannan safiyar ma'aikatar ta ce a shirye take na ta kare kasar daga duk wani hari da mayakan na Huthi ke shiryawa.

Wannan harin dai na zuwa ne mako guda bayan da mayakan Huthi suka dauki alhakin wani hari da ya hallaka mutane uku a Abu Dhabi, matakin da ya kai ga daura damarar sabbin hare-hare a tskanin tsakanin mayakan na Huthi da Hadaddiyar Daular Larabawa ya kara kamari.

Hadaddiyar Daular larabawa na daga cikin dakarun kawancen da Saudiyya ke jagoranta da ke yaki da mayakan Huthi a Sanaa.